An Karrama Babban Sakataren Hukumar Manyan Makarantun Sakandare Na Jihar Kano

Daga Ibrahim Muhammad

Cibiyar faɗakar da al’umma da bunƙasa cigaban jagoranci Centre For Public Enlightenment And Leadership Development, ta karrama babban Sakataren a Hukumar manyan makarantun Sakandire na jihar Kano, Alhaji Rabiu Saleh Gwarzo sakamakon yabawa da ayyukansa.

Karramawar da aka gudanar a ɗakin taro na makarantar koyon harshen Larabci SAS ta Kano a ranar Laraba ya sami halartar shugabannin makarantun Sakandare da ƙungiyoyi da ‘yan’uwa da abokan arziƙi.

A jawabinsa bayan karɓar shaidar karramawar babban Sakataren na Hukumar makarantun Sakandare na jihar Kano, Alhaji Rabi’u Saleh ya gode wa Allah bisa karramawar da Cibiyar ta yi masa bisa la’akari da abin da gani suka karrama shi kamar yadda suka faɗa.

Ya yi nuni da cewa amma shi gani yake kamar a wuri ɗaya yake bai ga ya yi wani abu da ya cancanci wannan karramawar ba, amma tunda sun gani suna gode musu da abin da suka hango da fatan Allah ya ƙarfafa masa gwiwar cigaba da ya yi fiye da abin da suka shaidi yana yi.

Alhaji Rabi’u Saleh Gwarzo ya ce zuwan gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf an samu cikakken gyara a hukumar manyan makarantun Sakandare da aka fi sani da Gidan Malamai da a duk ma’aikatun jihar Kano Hukumarsu ce a gaba wajen yi wa Malaman Sakandire ƙarin girma da kyautata musu.

Alhaji Gwarzo ya ce matuƙar burinsa a matsayinsa na Shugaban Hukumar makarantun Sakandare na jihar Kano shi ne ya samar da yanayi na ingantaccen ilimi da tarbiyya a makarantu su koma cikin yanayi mai kyau da walwala da za su gina cigaban ilimi mai inganci.

Shi ma a nasa jawabin, Daraktan cibiyar faɗakar da al’umma da bunƙasa cigaban jagoranci, Malam Auwal Yalwa ya ce sun karrama babban Sakataren na Hukumar makarantun Sakandare na jihar Kano, Alhaji Rabi’u Saleh Gwarzo ne bisa la’akari da irin ƙwazon sa tun zuwan sa Hukumar ma’aikata tun daga malamai har kan masu gadin makarantu suna samun natsuwa, haka daraktoci ana bai wa kowa damar aikinsa da su da malamansu.

Ya ce don haka Cibiyar tasu ta ga ya cancanci ta karrama shi domin ƙarfafa gwiwarsa a kan aikin da yake na bunƙasa cigaban malamai da makarantun Sakandire na jihar Kano.

Malam Auwal Yalwa ya yi kira ga shugaban makarantun Sakandire da malamai a kan su riƙe aikinsu da gaskiya domin Allah ya bai wa Hukumar Uba nagari jajirtacce mai son cigabansu wanda zuwan sa Hukumar ta sami gata ana aikace-aikace na kyautata musu.

Shi ma da yake jawabi, ɗaya daga cikin mahalarta taron a madadin tsofaffin ɗalibai na Kwalejin Ilimi na Kano ‘yan aji na 1996, Alhaji Muhammad Babagana ma’aikaci a Hukumar masu yi wa ƙasa hidima ta jihar Kano sun taya babban Sakataren Hukumar Kula da manyan makarantun Sakandare murna.

Alhaji Muhammad Babagana ya ce, “Alhaji Rabi’u Saleh Gwarzo tun suna makaranta mutum ne shi na jama’a mai ƙwazo da jajicewa da kyatatawa da hidimtawa a tsakaninsu. Duk da wannan matsayi da yake a kai, amma yana tare da mu.”

A yayin taron an karrama wasu daga cikin shugabannin makarantun Sakandare saboda ƙwazonsu.

  • Related Posts

    Mataimakin Gwamnan Kano Ya Halarci Taron Maulidin Manzo (S) da Hon. Muktar Ishaq Ya Saba Shiryawa A Yakasai

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Murtala Sule Garo, ya yi kira ga al’ummar Musulmi, musamman matasa, da su yi koyi da rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad…

    Iyayen Yara Sun Yaba Wa Makarantar Al-Burhan International College Bisa Yaye Mahaddata Al-Qur’ani Karo Na Huɗu

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Al-Burhan International College da ke Bayan Wailaki a Jihar Kano, ta gudanar da bikin yaye mahaddata Al-Qur’ani karo na hudu. Da yake bayani kan kafuwar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength