Daga Ibrahim Muhammad Kano
An rantsar da sabbin shugabannin Kungiyar Shugabannin Makarantun Sakandare ta Jihar Kano, ANCOPSS, tare da raba magunguna ga makarantun kwana na jihar Kano.
A yayin taron, Sakataren Gudanarwa na Hukumar Kulada Makarantun Sakandare ta Jihar Kano, Alhaji Rabiu Saleh Gwarzo ya yi kira ga wadanda aka rantsar da su mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi shugabancin makarantu. Ya kuma jaddada bukatar su zama “tsintsiya madauri daya” saboda yana da riba da yawa.
idan aka samu hadin kai, za a ga tasirinsa wajen inganta makarantu da cigaba da bada gudunmuwa
Alhaji Rabiu Saleh ya taya sabbin shugabanin murna, tare da yi musu alkawarin ba su cikakken hadin kai wajen ganin an tafi tare an tsira tare domin samun nasara a makarantun.sakandiren jihar Kano.
Da yake bayani kan rabon magunguna ga makarantun kwana, Hon. Rabiu Saleh Gwarzo ya ce wannan mataki ne na koyi da kokarin Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da irin kulawar da yake bai wa harkar ilimi.
Ya bayyana cewa yawancin makarantun kwana na da nisa da garuruwa, kuma idan rashin lafiya ta samu dalibai, sai an dauke su zuwa wuri mai nisa kafin a ba su magani.
“Saboda haka ne muka samar da wadannan kayayyaki domin su taimaka wajen ba da agajin gaggawa kafin a kai dalibin asibiti domin samun cikakkiyar kulawa,” inji shi.
Ya bayyana cewa makarantun kwana 20 ne za su amfana da wannan tallafin na magunguna. Ya kuma ja hankalin shugabannin makarantun da su yi kyakkyawar kulawa da magungunan, da kuma bai wa duk wani dalibi da ya samu larura kulawar gaggawa.
A nasa bangaren, sabon Shugaban ANCOPSS na Jihar Kano kuma Shugaban Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Dala, Kwamared Halliru Inuwa ya bayyana farin cikinsa da rantsar da su. Ya ce za su bada gudummuwa wajen cigaban kungiyar.
Ya jaddada cewa babu abin da ya fi muhimmanci gare su kamar hadin kai tsakanin shugabannin makarantun sakandare na jihar Kano, domin tabbatar da cimma manufofin gwamnati a makarantu.
Shugaban na ANCOPSS Kwamared Halliru Inuwa yace ba wata kungiya da zata cigaba sai da karbar shawara. Don haka kofar sa za ta kasance a bude ga shawarwari masu amfani. Suna bukatar hadin kai domin su ne masu bai wa dalibai tarbiyya. Idan suka hada kai duk abin da aka sa a gaba za su hadu su tabbatar ya yi nasara







